13 Agusta 2015 - 15:28

Kungiyat Yan ta'adda ta ISIS ta dauki alhakin harin da aka kai a kasuwar Jmaila a bienin Sadr na kasar Iraki a yau Alhamis kuma ya yi sanadiyar shahadar mutane sama da 30 tare da jikka wasu Daruruwa, kuma wasu 17 na daban sun bace saboda kidimewa da suka yi.

Wata mota shakare da bama-bamai ta tarwaste a wata Kasuwa a birnin Sadr na kasar Iraki kuma ta yi sandiyar shahasar sama da mutum 30 da kuma jikkata daruruwa.

Rahotani da suka fito daga kasar Iraki sun nuna cewa kungiyar yan ta’adda ta ISIS ta dauki alhakin harin da aka kai a kasuwar Jamila dake birnin Sadar a yau da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 30 tare da jikkata wasu daruruwa,

Ita dai wannan mota shakare da bamabami ta tarwaste ne a daidai lokacin da mutane ke cin kasuwa lamarin da ya jefa mutane cikin firgici da kidimewa inda yanzu haka ma kimanin mutane 17 ne suka bace ba a gansu ba. Ana ta bangaren majalisar ministocin kasar ta dage zaman da ta shirya yi a yau har sai abin da hali yayi.A